Jamus: Puigdemont ya fice daga gidan kaso
April 6, 2018Talla
Wata kotu a Jamus ta bayyana a ranar Alhamis cewa ta yi fatali da bukatar a mayar da tsohon jagoran yankin na Katalioniya zuwa Spain bisa laifi na yi wa mahukunta tawaye a lokacin kamfe na neman yankinsa ya samu 'yancin gashin kai daga Spain sai dai kotun ta ce za ta iya duba bukatar mahukuntan na mayar da shi gidan bisa wasu laifukan da ke zama kanana kamar almubazzaranci da kudaden al'umma. Puigdemont ya fice daga gidan kaso da ake tsare da shi a Jamus bayan cika wasu sharuda da suka sanya aka sake shi.
Tuni mahukuntan Spain suka ce za su mutunta hukuncin da kotun Jamus ta yanke. Mai magana da yawun gwamnati a Spain Inigo Mendez de Vigo ne ya bayyana haka a wannan rana ta Juma'a wajen taron manema labarai da ya saba yi a duk mako.