Haraji a kan masallatai a Jamus
December 27, 2018Talla
Gwamnatin Jamus ita ce ke cire harajin wa mabiya al 'ummar Kirista, amma kuma daga baya kudaden da ta zabtaren na harajin ta zubasu ga hukumomin kula da Cocina domin gudanar da aikace-aikacen na Cocin. Thorsten Frei, wani na kusa da shugabar gwamnatin Angela Merkel ya ce girka haraji zai kara ba da dama wajen habakar Musulumcin a Jamus, sakamakon tallafin da hukumomin addinin Musuluncin za su rika samu daga gwamnatin Jamus don gudanar da aika-aikace na masallatai.