1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Erdogan ya bude masallaci a Kolon

Gazali Abdou Tasawa
September 29, 2018

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya kammala ziyararsa a kasar Jamus tare da kaddamar da wani babban masallaci a birnin Kolon

https://p.dw.com/p/35iPs
Deutschland Erdogan Besuch in Köln
Babban masallaci da aka bude a KolonHoto: DW/W. Glucroft

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya kammala ziyararsa a kasar Jamus tare da kaddamar da wani babban masallaci a birnin Kolon. Masallacin wanda wata kungiyar kasar ta Turkiyya mai suna Ditib ta dauki nauyin ginawa, na zama masallaci mafi girma a Jamus.

Sai dai dubban jama'a masu adawa da ziyarar shugaban Turkiyyar sun gudanar da zanga-zanga a birnin na Kolon inda aka tsaurara matakan tsaro.

A lokacin ziyarar tasa, Shugaba Erdogan ya yi kira ga kasashen Turai da kara kaimi wajen yaki da ta'addancin kungiyar 'yan awaren PKK da kuma magoya bayan Fethullah Güllen wanda Turkiyar ke zargi da kitsa juyin mulkin shekara ta 2015 da bai yi nasara ba.