Jamus: An kama hanyar kafa gwamnatin hadaka
February 7, 2018Batun 'yan gudun hijira musamman ma dai wanda ya shafi sake hadewar iyalansu da suka taka rawa a tattaunawar kafa gwamnatin kawance ya sake kunno kai a jawabin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi. Kamar yadda ta saba a baya Merkel ta ce za su yi duk mai yiyuwa don kare rayuwar al'ummar kasa da kuma daukar matakan da suka dace kan bakin haure:
"An san cewa kasar mu kasa ce mai alfahari da irin karfin tattalin arzikinta, za mu samarwa al’umma abubuwan more rayuwa dama tsaro kamar yadda muke son inganta tsaron cikin gida. Daya daga cikin damuwarmu dai ita ce magance matsalar kwararar baki da kuma zaunar da su a cikin kasar. Mun cimma yarjejeniyar kwarai , wanda bai zo da sauki ba sai dai mun cimma matsaya sahihiya.''
Shi da kansa jagoran jam'iyyar ta SPD Martin Schulz wanda jam'iyyarsa ta zo na biyu lokacin zaben watan Satumbar da ya gabata, wanda daga bisani ya yi ammai ya lashe a game da wasu dalilai na kin kafa gwamnatin hadaka a farko ya ce a kokarin hana Jamus fadawa cikin matsala ta siyasa a dalilin rashin kafa gwamnati musanman na janyo cikas ga zamanta a kungiyar Tarrayar Turai da ke kokarin kaddamar da sauye-sauye na tattalin arziki a jawabin na sa ya karkata hankalinsa kan batun na EU da cewa:
"Wadannan sauyin za su zama zahiri, ina fatan ganin hakan, a dalilin wannan hadaka za mu karfafa dangantaka da Paris don karfafa kungiyar Tarrayar Turai a kokarin fuskantar barazanar tsaro da duniya ke ciki da batun yarjejeniyar sauyin yanayi da kuma matsalar kauce biyan haraji da kuma kasuwa ta bai daya da ya shafi tattalin arzikin Jamus. Wannan zai bai wa Jamus karfi da kariya da ta ke bukata daga kungiyar tarrayar turai."
Shi kuwa Horst Seehofer da ya sha adawa da matakin Merkel inda ya bukaci ta taka birki ga shirinta na tarbar baki a Jamus, yabawa ya yi yau da yarjejeniyar a abinda ya kira dinke baraka da aka samu na rarrabuwar kanu don ci gaban kasa.
Ya ce "Duk wanda ya karanta takardun yarjejeniyar, wanda na ke fatan mutane da dama za su yi, za a gani muna da shirye shirye da dama don inganta rayuwar al’ummar kasar nan, hadakar za ta magance matsalar rarrabuwar kannun don haka na ke cewa yarjejeniyar abu ne da ke da tasiri matuka.’’
Abinda ya rage a yanzu dai shi ne, tilas ne a jira wakilan jam'iyyar ta SPD har su 460,000 su kada kuri'ar amincewa kafin a kafa gwamnatin hadakar ta Jamus tsakanin manyan jam'iyyun kasar.