1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: A daina nunawa Beijing wariya

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 22, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci kasashe masu karfin tattalin arziki na yammacin duniya, su dama da Chaina cikin tsarin kasuwancinsu.

https://p.dw.com/p/3Wezo
Deutschland Libyen-Konferenz in Berlin
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Reuters/A. Schmidt

Merkel dai ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kyautar da ta karba a makarantar Amirka da ke Berlin, inda tace kin damawa da Beijing din ka iya janyo yakin cacar baka tsakaninta da kasashen na Turai. Taron karrama Merkel din dai, ya samu halartar tsofaffin sakatarorin harkokin kasashen ketare na Amirka Henry Kissinger da John Kerry. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta nunar da cewa ci-gaban tattalin arzikin Chaina na fuskantar kalubale:

"A yanzu kamata ya yi mu yi tunanin yadda za mu bullowa wannan kalubalen. Kamar yadda na yi a farko muna bukatar kyakkyawar alakar ksuwanci tsakanin Amirka da Turai, dan haka zan yi kokarin ganin an kulla wannan dangantaka mai karfi, a lokiacin da na ke shugabar gwamnati da ma bayan na bari. Wannan kyauta da aka bani za ta karfafa min gwiwa, na gode da karramawa." 

Merkel dai na shirin shirya wani taron Jamus da Chaina nan da tsakiyar wannan shekarar, yayin da Jamus din za ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar Tarayyar Turai EU na watannin shida-shida.