Jammeh ya fara gudun hijira a kasar Equatorial Guinea
January 22, 2017Talla
Mutumin da tun farko ya ki sauka daga mulki duk da kaye da ya sha a zaben ranar 1 ga watan Disamba, Jammeh ya yi sanadiyyar tayar da jijiyar wuya da yunkurin daukar matakin soja, da nufin tilasta shi bawa sabon shugaban kasar Adama Barrow madafan iko.
Tsohon shugaban na Gambiya tare da rakiyar Shugaba Alpha Conde na Guinea sun bar birnin Banjul a wani karamin jirgin sama zuwa Conakry babban birnin Guinea kana daga bisani ya shige kasar Equatorial Guinea, inda zai yi zaman gudun hijira, a cewar shugaban kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza a birnin Dakar.