Jam'iyyar SPD ta sadaukar wa Olaf Scholz takararta
January 11, 2025Jam'iyyar SPD ta sake tsayar da shugaban gwamnatin Jamus mai ci Olaf Scholz a matsayin dan takararta a zaben gabanin wa'adi da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.
Karin bayani : Shugaban gwamnatin Jamus ya caccaki mai kamfanin X Elon Musk
A taron da jam'iyyar ta gudanar a birnin Berlin, wakilan jam'iyyar ta Social Democrats (SPD) sun kada kuri'ar amincewa da takarar Olaf Scholz in ban da kalilan da suka nuna adawa da hakan.
A jawabin amincewa da takarar, shugaban gwamnati mai barin gado Olaf Scholz, ya ce Jamus na cikin dambarwar siyasa.
Shugaban ya kuma ce akwai bukatar samar da daidaito a batun haraji da gidaje da kuma tsarin fansho mai nagarta ga wadanda suka yi ritaya.
Karin bayani : Jamus ta shiga sabuwar shekara da batun zabe
Olaf Scholz ya kuma yi zargin jam'iyyun hadakar kasar da ke gaba-gaba wajen hamayya da gwamnatinsa CDU/CSU wajen yin kafar ungulu a dukkan al'amuran da suka shafi ci gaban siyasa.