Adamawa: APC ta soki ranar sake zaben gwamna
March 27, 2019Talla
Jamiyyar APC mai mulki a jihar Adamawa ta bayyana rashin amincewarta da ranar da hukumar zabe ta tsayar domin ci gaba da zaben gwamna a mazabu 44 na jihar.
Sakataren gudanarwa na jamiyyar Ahmed Lawan ne ya sanar da matsayin jamiyyar a Yola.
Jamiyyar ta yi watsi da ranar Alhamis 28 ga wannan watan na Maris da hukumar zaben ta sanar domin gudanar da zaben bisa hujjar cewa ba’a tuntube su ba kafin tsayar da ranar.
Hukumar zabe mai zaman Kanta ta Najeriya, INEC ta tsayar da ranar 28 ga watan Maris domin gudanar da zaben gwamnan jihar Adamawan a mazabun 44 da ke kananan hukumomi 14 na jihar.
Masu jefa kuri’a dubu 40,988 ne za su yi zaben wanda zai kai ga fitar da wanda zai yi nasara a matsayin gwamnan jihar ta Adamawa.