Jam´iyar shugaba Putin na kan gaba a zaɓen Rasha
December 3, 2007Kakakin fadar Kremlin a birnin Mosko ya ce sakamakon farko na zaɓen ´yan majalisar dokoki da aka gudanar yau ya yi nuni da cewa ´yan Rasha sun goyi da bayan manufofin shugaba Vladimir Putin tare da neman da a ci gaba da bin wannan tafarki. Mutane dai sun fita ƙwansu da kwarkwatansu don kaɗa ƙuri´a a zaɓen na yau. Kamar yadda kamfanin dillancin labarun Interfax ya nunar yawan waɗanda suka kaɗa ƙuri´a ya kai kashi 56 cikin 100 idan aka kwatanta da shekaru huɗu baya. Mutane kimanin miliyan 108 suka cancanci kaɗa ƙuri´a a zaɓen na Rasha inda jam´iyu 11 suka tsaya takara. Ƙuri´ar jin ra´ayin jama´a ta yi nu ni da cewa jam´iyar shugaba Vladimir Putin ka iya samun kashi 60 cikin 100 na yawan ƙuri´un da aka kaƙa. Wata ƙungiyar Rasha mai zaman kanta dake sa ido a zaɓe wato Golos ta ce an yi aringizon ƙuri´u a wurare da dama. Su kuma ´yan adawa sun yi ƙorafi game da tursasa musu da kuma satar ƙuri´u.