Rudani bayan dafifin jami'an tsaro a majalisar Najeriya
August 7, 2018Jami'an tsaro na farin kaya na ci gaba da toshe kofar shiga majalisar dokokin Najeriya inda suka hana daukacin ma'aikata da ‘yan jaridu shiga majalisar abin da ya haifar da takaddama mai zafi tare da tilasta dage taron da shugabanin majalisar suka tsara gudanarwa bisa zargin yunkuri na tsige shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki.
Tun talatainin dare ne dai jami'an tsaro suka yi wa majalisar kawanya abin da ya haifar da taruwar jama'a. An dai tsara za a gudanar da taro ne na shugabanin majalisar domin yiwuwar sake budeta don amincewa da kasafin kudin hukumar zabe da shugaban Najeriyar ya gabatar. Hatta ‘yan majalisa dai sai da suka taka a kafa don shiga majalisar. Hon Ismaila Muazu Hassan dan jam'iyyar PDP ne ya bayyana bacin rai a kan abin da ya faru.
‘Ya'yan jamiyyar PDP dai na ta kai kawo a kan shugabancin majalisar da ya koma hannun jam'iyyar adawa ta PDP bisa cewa ba za ta sabu ba, domin su ke da rinjaye, abin da ke haifar da zargi na yunkurin amfani da karfi wajen tsige shugabanta Bukola Saraki. To sai dai ga Hon. Muktar Muhammad Ciroma na mai bayyana bukatar fahimta a lamarin.
Kungiyoyin kare hakkin jama'a dai sun yi dafifi a gaban majalisar a bisa abin da suka kira kokari na kare dimukuradiyyar Najeriyar. Dr Usman Muhammad shugaban kungiyar kula da harkokin 'yan majalisa na mai bayyana hatsarin da ke tattare da wannan.
Ta dai kai ga ihu ga duk wani wanda ya yi kokarin jawabi na nuna goyon baya daga kungiyoyin matasa. Duk da dage wannan taro da alamun tsugune bata kare ba, musamman yadda manyan jam'iyyun biyu ke ci gaba da sauya sheka a kokari na samun rinjaye da ma darewa kan shugabancin majalisar.