1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami´an tsaro a Nigeria sun fara aiwatar da umarnin Obasanjo

August 16, 2006
https://p.dw.com/p/BumY

Jami´an tsaro a Nigeria sun kaddamar da gagarumin shirin lalubo tsagerun yankin Niger Delta dake ci gaba da rike ma´aikatan man nan na kasashen ketare guda biyar.

A cewar kakakin rundunar jami´an yan sanda na Nigeria, wato Mr Hanz Iwendi sun dauki wannan matakin ne, don ceto wadannan mutane tare da kawo karshen wannan matsala a yankin baki daya.

Yankin na Niger Delta , yanki ne da yayi kaurin suna wajen fuskantar tashe tashen hankula da kuma yawaitar yin garkuwa da fararen fatu dake aiki a kamfaninnikan hakar mai dake yankin.

Idan dai za a iya tunawa, a jiya ne shugaba Obasanjon ya bayar da wannan umarni ga rundunar yan sandan ta Nigeria, a kokarin da gwamnatin sa keyi na inganta harkokin tsaro a fadin kasar baki daya.