Jami'an tsaro a kasar Jamus sun cafke wasu mutane
March 18, 2018Talla
Sanarwar ta kara da cewar sama da mutane dubu 11 ne suka gudanar da zanga-zangar tare kuma da jifan jami'an 'yan sandan Jamus da robobin ruwa da yi musu barazanar zane su da sandan tutocin da suke rike dasu yayin zanga zangar. Masu gudanar da zanga-zangar sunyi korafi akan cinikin makamai tsakanin Turkiyya da kuma kasar ta Jamus tare kuma da kiran shugaba Recep Tayyip Erdogan dan Ta'adda.
.