Jama'a na yin tir da hare-hare a Borno da Yobe
November 2, 2023Baya ga harin da Kungiyar ISWAP ta kai inda ta halaka mutane 40 a jihar Yobe wanda shi ne mafi muni a watanni 18, ita ma Kungiyar Boko Haram ta halaka wani limami da na'ibinsa gami da wani jami'in tsaro a Karamar hukumar Kaga ta jihar Borno. Haka kuma mayakan na Boko Haram sun halaka wasu mutane a karamar hukumar Bama a jihar Borno tare da kame matafiya da dama a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, abn da aka kwashe kusan shekara guda ba a gani ba a wannan hanyar. Dawowar wadannan hare-hare sun dagulawa al'ummar wannan yankin lissafi bayan da suka fara sakin jiki, ganin cewa an samu zaman lafiya na tsawon lokaci.
Idris Baffa Geidam, wani dan yankin da aka kai wadannan hare-hare a jihar Yobe ya bayyana cewa: " Akwai fargaba ga mutanen da suke zaune a kauyukan da ke karamar hukumar Geidam musamman ma gabashi da kudancin Geidam. Gaskiya mutanen da suke wadannan kauyuka na zaman fargaba da zullumi sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.”
Karin bayani:Hare-hare na illata sana'o'i a yankin tafkin Chadi
Shi kuma Ahmad Usaini ya nuna damuwa kan abin da ya faru saboda babu wasu hukumomi da suka kai musu tallafi ko makamantansu. A nasu bangaren, masana da masharhanta na na cewa ba su yi mamakin samun wadannan nan hare-hare a wannan lokaci ba saboda an saki jiki duk da cewa ba kare wannan yaki ba.
Dr Lawal Jafar Tahir, Shehin malami a jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu ya ce: " Yaki ne na sunkuru kuma za a iya shammatar mutane a kowane lokaci. Wadannan yaran sun zauna a jejin nan ba wai sun bar wannan abin ba ne, saboda haka ya faru. Yawancin masana bai zo musu da mamaki ba saboda sun dade suna sharhi a kan cewa wannan bai kare ba, gara a sake daukar mataki..”
Karin bayani:'Yan Najeriya sun ce ba a murkushe ta'addanci ba
Jami'an tsaro sun ce suna daukar matakai da suka kamata na ganin an magance wadannan hare-hare da mayakan na Boko Haram ke kaiwa. Babban Hafsan tsaro na Najeriya Janar Christ Musa ya ce ya kamata mutane su bai wa jami'an tsaro hadin kai da ya kamata domin dorewar nasarar da aka sa a gaba. Yanzu haka dai an shaida ganin karuwar matakan tsaro a kan hanyoyin wannan shiyya ganin cewar ana fuskantar matsala lokacin tafiye da kuma bukuwan karshen shekara.