1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakob Zuma ya gana da Goodluck Jonathan

April 16, 2013

Najeriya da Afirka ta Kudu sun kuduri aniyar karfafa ma'amala tsakanin su.

https://p.dw.com/p/18H1D
Nigeria's President Goodluck Ebele Jonathan (L) and South Africa's President Jacob Zuma attend the annual meeting of the World Economic Forum (WEF) in Davos January 23, 2013. REUTERS/Pascal Lauener (SWITZERLAND - Tags: POLITICS BUSINESS)
Hoto: Reuters

A wani abun dake zaman kama hanyar danyen ganye a tsakanin kasa mafi karfin tattalin arziki da 'yar uwarta mafi yawan jama'a a nahiyar Afirika baki daya, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya kawo wata ziyarar aiki a Abuja

Daya dai na zaman giwa ga batu na tattalin arzikin nahiyar daya kuma nayi wa kanta kirarin bangon gabas matarar ruwa ga daukacin bakar fata a duniya baki daya.

A baya dai duk biyun sun kai ga kokarin kai ruwa a cikin rana dama kokari na gwanjin 'yar kwanji da nufin tabbatar da tasirin junansu kafin daga baya wani harin da ya bude sabon babi a cikin tarihin dayar ya kai ga sake hade kan kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu da shugabanninsu suka gana a Abuja suka kuma ce sun amince da nufin aikin tare domin kawo karshen matsolin rashin tsaron da nahiyar ta Afirka ke ciki.

A wata ziyarar wuni guda a Abuja dai ,Jacob Zuma bai yi wata wata ba wajen bayyana tsallen murnansa kan sabon kawancen da ya kama hanyar sake bunkasa tattalin arzikin kasar ta Afirka ta Kudu,sannan kuma ke shirin samar da dubban aiyuka a tsakanin matasa a sassa daban-daban na Tarayyar Najeriya.

18.03.2013 DW online Karte Nigeria Kano eng

Duk da cewar dai Najeriya ta kai ga tabbatar da kawo karshen mulkin wariyar kasar Afirka ta Kudu shekaru kusan 20 din da suka gabata, danyen ganye a tsakanin kasashen biyu dai ya bushe yayin da Afirka ta Kudun da tsohuwar kawarta ta Najeriya suka rika daukar matsayin hannun riga game da batun siyasa da ma mulki a cikin nahiyar.

Alal misali dai Afirka ta Kudun ta nemi tsaiko ga kokarin kasashen ECOWAS da Tarrayar Najeriya ke yiwa jagora suka nemi tabbatar da mulkin Alassan Ouattara bisa Laurent Gbabo shekaru kusan ukun da suka gabata,

abun kuma har da ya kai ta ga tura jirgin yaki ya zuwa gabar ruwar Abidjan ya kuma tada hankalin kasashen yankin.

Ko bayyanan dai an cigaba inda Tarayyar Najeriya tace sai Jean Ping ga kujerar shugaban Hukumar Gudanarwar Kasashen Nahiyar Afirka ta AU a yayin kuma da Afirka ta Kudun tayi nasarar dora tsohuwar ministar harkokin wajenta kuma tsohuwar mai dakin shugaba Zuma bisa kujerar dake matukar tasiri a cikin nahiyar a yanzu haka.

South African President Jacob Zuma delivers a speech on November 15, 2012, in the Parliament in Cape Town. Zuma hit back at accusations he is failing the country before a raucous parliamentary hearing today, hours after allies torpedoed attempts to censure him. Facing accusations he mismanaged the economy, was AWOL during deadly labour unrest and wasted millions of taxpayers' money on upgrading a private residence, a visibly angered Zuma struck back. It was a rare flash of steel for the normally jovial leader. In one month Zuma faces the ANC's electoral conference, which will go a long way toward deciding whether he remains president of Africa's largest economy for another five years. AFP PHOTO / STRINGER (Photo credit should read STRINGER/AFP/Getty Images)
Hoto: Stringer/AFP/Getty Images

To sai dai kuma harin ranar yancin kan Tarayyar Najeriya na shekara ta 2010 dai ya kai ga zamowar dan bar hada kai a tsakanin manyan kasashen biyu inda Afirka ta Kudun ta amsa bukatar Najeriya ta kuma kai ga kame dama tabbatar da hukuncin kan tsohon madugun kungiyar MEND mai fafutuka Henry Okah.

Bangarorin Biyu dai na kallon ziyarar ta Jacob Zuma a matsayin wani kokari na kara dinkin sabon zumuncin dake kara ganye da fulawa da a cikin sa manyan kamfanonin saye da sayar kasar ta Afirka ta Kudu ke tururuwar maye gurbin na turawan yamman da tauraruwarsu ke dusashewa.

Zuma ya ce mun yi imani a tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu akwai bukatar hada matsayi kan batutuwan da suka shafi makomar nahiyar Afirka baki daya . Musammam ma ga batun tsaro a nahiyarmu. Kamar yadda kuka sani akwai matsaloli a wasu kasashen nahiyar mun tattauna kan wannan. Kuma kun san nan gaba kadan Kungiyar Hada kan Kasashen Afirka zata yi bikin cikar ta shekaru 50, kuma akwai bukatar mu kalli ina muke kuma ina ya kamata mu kama hanyar zuwa. Ina jin mun samu tattaunawa mai amfani.

Ta fannin na tsaro dai kasashen biyu na da sojojin su a jibge a yanzu haka a kasashen Afirka ta Tsakiya da kuma Mali, inda suke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

A cikin watan gobe na mayu ne dai ake sarar shima shugaban kasar ta Najeriya zai gudanar da wata ziyar aikin a birnin Durban, ziyarar kuma da zata tabbatar dinkewar kasashen da yanzu haka ke nuna alamun shugabanci a cikin nahiyar taAfirka ziyarar kuma da a cewar babban mashawarcin shugaban Najeriya kan batu na siyasa Ahmed Ali Gulak ke nuna alamun karshen rikicin da shekarar bara ya kai ga tilasta ban hakurin mahukuntan kasar ta Afirka ta Kudu kan koro wasu 'yan kasar da basu da takardun shiga kasar cikkaku.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabuwar dangantakar ga nahiyar da har yanzu ke zaman ta kan gaba ga fatara da talauci kuma ke zaman mattatarar rigingimu iri-iri.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani