Wakilin Amirka a Afganistan ya bar aiki
October 19, 2021Talla
Wasu daga cikin 'yan kasar Afganistan na zargin babban jami'in diflomasiyyar Washington da ya yi murabus a mastayin wanda ya taimakawa kungiyar Taliban samun nasarar kwace iko da gwamnati a farkon watan Agustan 2021.
Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta tabbatar da murabus din Khalilzad, sai dai da yake maida martani kan wannan mataki, tsohon babban jami'in leken asirin Afganistan Rahmatullah Nabil ya kwatanta Khalilzad a matsayin mutumin da ya jefa kasar Afganistan cikin bala'in da ba za su iya fita ba.