1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jajircewar Mubarak a kan kujerar mulkin Masar

Anthony DunhamFebruary 2, 2011

Shugaban Masar ya ce ko ana ha maza ha mata ba zai sauka daga karagar mulki ba, sai wa'adin mulkinsa ya ƙare, kuma an gudanar da sabon zaɓen shugaban ƙasa a watan Satumban 2011.

https://p.dw.com/p/108tG
Hosni Mubarak lokacin da ya ke jawabi ga al'uma kasarsaHoto: AP

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da da riƙe madafun iko matiƙar wa'adin mulkinsa bai ƙare ba, ko da matsin lamba da ya ke ci gaba da sha zai ninka wanda ya ke fama da shi yanzu haka. A lokacin da ya yi wa al'umar ƙasarsa jawabi ranar Talata da maraice ta kafar talabijin, Mubarak ya ce zai iya sauka daga karaga ne kaɗai bayan zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa.

Sai dai masu boren na ci gaba da shan alwashin hamɓarar da gwamantinsa ta hanyar ci gaba da matsa ƙaimi, a wasu manyan biranen ƙasar baya ga Alƙahira, da Alexandiriya. Wasu jam'iyun siyasar ƙasar ciki kuwa har da ta 'yan uwa musulmi suka ce ba za su amsa kiran da Mubarak ya yi musu ba, na sansantawa tsakaninsu da nufin ci gaba da kakkange madafun iko .

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana cewa lokaci ya yi da shugaban na Masar da ya shafe shekaru talatin akan karaga, zai san inda dare ya yi masa. Tsohon shugaban hukumar makamshin nukilya ta ƙasa da ƙasa (IAEA) wato Mohammed El Baradei da ake ɗauka yanzu haka jagoran tayar da ƙayar bayan, ya danganta zanga-zangar da za su gudanar ranar juma'a da wacce za ta bayar da damar fatattakar Mubarak daga mulki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas