1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan adawa zai yi takara a zaben Guinea

Fréjus Quenum | Mouhamadou Awal Balarabe SB
June 14, 2023

Shugaban jam'iyyar UFDG kuma madugun adawa na Guinea Conakry Cellou Dalein Diallo ya bayyana aniyar tsayawa takara a zabe mai zuwa, duk da kwashe sama da shekara guda yana gudun hijira bisa dalilai na siyasa.

https://p.dw.com/p/4SYlW
Cellou Dalein Diallo FNDC
Cellou Dalein Diallo jagoran 'yan adawa na kasar GuineaHoto: Sadak Souici/Zumapress/picture alliance

A cikin wata hira ta musamman da ya yi da DW, dan siyasan ya zargi shugaban mulkin soja Mamadou Doumbouya da rashin damawa da kowa da kowa don samar da kundin tsrain mulki da zai dora kasar kan kyakkyawan tafarki.

Karin Bayani: Siyasar Guinea ta dagule

Gwamnatin mulkin sojan Guinea na shirin samar da sabon kundin tsarin mulki da nufin mayar da kasar kan tafarkin dimukaradiyya, inda take tuntubar bangarorin siyasa da na farar hula don neman gudunmawarsu. Sai dai duk da cewa fadar mulki ta Conakry ta bayyana aniyar tattaunawa da kowa da kowa da nufin gudu tare don tsarira tare, amma ta nemi mayar da madugun adawa Cellou Dalein Diallo na jam'iyyar UFDG saniyar ware. Amma dai Diallo ya ce ba za ta sabu ba, duk da cewa shugaban gwamnatin mulkin soja Mamadou Doubouya ya raba kawunan 'yan Guinea don neman dauwama a kan mulki.

Cellou Dalein Diallo
Cellou Dalein Diallo jagoran 'yan adawa na kasar GuineaHoto: Sadak Souici/Le Pictorium Agency/ZUMA/picture alliance

Cellou Dalein Diallo dai yana gudun hijira tun watan Afrilun 2022,  kuma yanzu haka yana rangadin kasashe da dama musamman ma na Turai, lamarin da ka iya mummunan tasiri a yunkurinsa na tsayawa takara a zabe mai zuwa a Ghuines Conakry. Sai dai dan siyasar ya ce so da kauna da magoya bayansa da fahimtar manufofin jam'iyyarsa da 'yan Guinea suka yi sun wadatar wajen ci gaba da raya sunansa a kasarsa ta haihuwa.

A shekarar 2024 ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa. Amma  babu wani yunkuri da Cello Dalein Diallo yake yi  hadan gwiwa da Alpha Condé, tsohon shugaban kasar Guines wajen ganin sun jera tare, inda tattaunawar karshe tsakanin bangarorin biyu ta gudana a shekarar da ta gabata.

Shekaru uku da suka gabata dai aka sabunta kundin tsarin mulkin Guinea, lamarin da ya ba wa Shugaba Alpha Condé damar yin tazarce da ya zama silla na yi masa juyin mulki. Amma kuma bai sa madugun 'yan adawa Cello Dalein Diallo dasawa da sabbin hukumomin mulkin sojan kasar ba.