Italiya na fargabar sake bullar corona
July 3, 2020Talla
A makon gobe ne dai hukumomin suka ce za su fidda sabbin dokoki a yankin wanda ya hada da Venice, kuma sun ce za su yi hakan ne da nufin dakile bazuwar cutar.
Wannan matakin da ake shirin dauka dai na zuwa ne bayan da aka sami wani mutum dauke da cutar da ya kuma ki ya kebe kansa, har ma ya kai ga yin mu'amala da muatnen da yawansu ya kai 89,
kuma tuni aka tabbatar da cewa hudu daga cikinsu sun kamu da cutar yayin da shi kansa yanzu haka yake kwance cikin mawuyacin hali.