1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'a na murna da sako ma'aikatan agaji

June 15, 2021

Al’umma a Maiduguri sun barke da murna bayan kungiyar Boko Haram bangaren ISWAP ta sako Ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya da ma’aiakatan agaji da ta yi garkuwa da su tsawon lokaci.

https://p.dw.com/p/3uz0d
Nigeria Soldaten patrouillieren in Tungushe
Hoto: AFP/Str

Ba zato ba tsammani aka sako Idris Aloma da ke aiki da Majalisar Dinkin Duniya wanda mayakan ISWAP suka kama a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da sauran ma’aikatan jinkai da suka kwashe tsawon lokaci.

Babu wasu dalilai da aka bayar na ya yadda aka yi aka sako su babu kuma bayanai da su ka nuna an biya kudin fansa amma rahotanni sun ce an yi tattaunawa kafin a sako su.

Dukkanin wadan da aka sakon din suna wajen jami’an tsaro domin tantance su da ma duba lafiyar su kafin hada su da iyalansu.

Wata ‘yar uwar wadanda aka saka mai suna Yana Ali ta bayana cewa ba za su iya misalta farin cikinsu ba don har sun fitar da tsammanin sake ganin ‘yan uwan nasu.

Suma ma'aikatan sun ji dadin sake abokan aikin su da aka kwashe lokaci ana garkuwa da su. Malam Isma’il Idris Hinna wani mai aikin jinkai ne a shiyyar Arewa maso gabashin da ya ke aiki da wasu daga cikin wadan da aka saka.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijira ma dai sun yi murna inda suka yi fatan Kungiyoyin da suka janye za su dawo aiki don ci gaba da taimaka musu.

Bukar Mustapha Damboa wani dan gudun hijira da ya yi fatan irin damar da aka samu za ta kai ga yin sulhu da mayakan na ISWAP bangaren Boko Haram don kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 12 ana fama da shi.