1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Daftarin tsaron Zirin Gaza

Suleiman Babayo ATB
February 23, 2024

Firaministan Isra'ila ya gabatar da jadawalin tsaron yankin Zirin Gaza bayan yaki da ke faruwa inda gwamnatinsa za ta karbi tafiyar da tsaron yankin.

https://p.dw.com/p/4cnvG
Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila
Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ilaHoto: Amos Ben-Gershom/dpa/picture alliance

Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya gabatar da taswirar farko a hukumance bisa tsarin yankin Zirin Gaza na Falasdinu bayan yakin da ke faruwa, inda gwamnatin Isra'ila za ta ci gaba da kula da harkokin tsaron duk yankunan Falasdinawa na yankin tare da sake gina Gaza da kawar da harkokin makamai a yankin baki daya.

Tsarin ya kuma kunshi cewa Isra'ila za ta ci gaba da tafiyar da tsaron yankin gabar yamma da kogin Jodan.

Tun ranar Talata da ta gabata Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya gabatar da daftarin ga majalisar tsaron kasa, wadda za ta iya kawo sauye-sauye ga matakan kuma a wannan Jumma'a kamfanin dillancin labaran Reuters ya ga kunshin daftarin na matakan da Isra'ila za ta dauka kan tsaron bayan yaki.