1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila za ta mikawa Falasdinu kudadenta

Ahmed SalisuApril 18, 2015

Mahukuntan Isra'ila sun ce za su mikawa Falasdinu kudinta kimanin miliyan dala miliyan 470 da suke rike da su bayan da bangarorin biyu suka cimma matsaya kan wannan batu.

https://p.dw.com/p/1FATh
Palästinenserpräsident Mahmud Abbas
Hoto: Reuters

Shugaban Falasdiwa Mahmud Abbas ne ya ambata hakan a wannan Asabar din inda ya ke cewar jami'an Isra'ila da Falasdinu din za su sake zama don tattaunawa kan batun sakin sauran kudin Falasdinun da ake rike da su.

Wani jami'in gwamnatin Isra'ila da ya zabi a sakaya sunansa ya ce an saki kudin ne don tabbatar da zaman lafiya a yankin, to sai dai bai yi karin haske game da hakan ba.

A watan Disambar da ya gabata ne Isra'ila ta fara rike kudaden haraji da ta ke karba da sunan Falasdinu bayan da Falasdinun ta sanar da aniyarta ta shiga jerin kasashen da ke zaman mabobi a kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki, yunkurin da bai yi wa Isra'ila dadi ba.