1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta haramta ayyukan UNRWA

November 4, 2024

Isra'ila ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, UNRWA bisa zargin hukumar da alaka da Hamas.

https://p.dw.com/p/4mYiv
Nahostkonflikt - UN-Hilfswerk für palästinensische Flüchtlinge
Hoto: Gehad Hamdy/picture alliance/dpa

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce, Isra'ila ta bayyana wa Majalisar Dinkin Duniya a hukumance cewa ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin Falasdinawa ta Majalisar UNRWA. A watan da ya gabata ne 'yan majalisar dokokin Isra'ila suka bukaci a haramta ayyukan hukumar a Isra'ila, da dakatar da dukannin wani hadin kai da Isra'ila ke bai wa hukumar da ake ganin a matsayin madogara ga miliyoyin Falasdinawa, da ke gabar yamma da kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

Karin bayani: Majalisar dokokin Isra'ila na shirin haramta wa MDD aikin agaji a Falasdinu 

Isra'ila dai ta zargi hukumar da rashin adalci da ma hannun wasu daga cikin ma'aikatanta a harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Octoban shekarar 2023. Ko da yake matakin ya takaita aikin hukumar a gabar yamma da kogin Jordan , sai dai hakan zai yi mummunan tasiri kan aiki jin kai na hukumar, wanda dama ke fuskantar kalubale na karancin kayan agaji a Gaza.