1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila: Kotun kasa da kasa za ta yanke hukunci kan Gaza

January 26, 2024

Kotun kasa da kasa da ke Hague za ta yanke hukuncin farko kan karar da kasar Afrika ta Kudu ta shigar gabanta na dakatar da Isra'ila kan hare-haren da ta ke kai wa Gaza da kuma bukatar shigar da kayan agajin gaggawa

https://p.dw.com/p/4bh5z
Hoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Babu tabbacin alkalan kotun na kasa da kasa da ke birnin Haque na kasar Nethérlands za su yanke hukunci kan batun zargin kisan kare dange da aka gabatar gabanta.

Karin Bayani: Kotun MDD zata fara shari'ar Pretoria da Isra'ila kan Gaza

Tun da fari dai,  an tsara cewa alkalan kotun za su yanke hukuncin na yau kan bukatar kasar Afrika ta Kudu na dakatar da Isra'ila daga hare-haren da ta ke kai wa Gaza domin kare rayukan Falasdinawa fararen hula.

Karin Bayani: ICC ta ce toshe agajin Gaza laifin yaki ne 

Afrika ta Kudu ta shigar da kara gaban kotun a karshen watan disamba bisa dogaro da yarjejeniyar kawo karshen kisan kare dangi da kasashen duniya suka rattaba hannu tare kuma da bukatar Isra'ilan da ta bari a shigar da kayayyakin agajin jin kai ba tare da shamaki ba.

Kasar ta Afrika ta Kudu ta kafa hujja ce da kalaman ministan Isra'ila na cewa za su shafe Gaza daga doron kasa.

Karin Bayani: Israila ta yi watsi da zargin kisan kare dangi a Gaza 

Isra'ila ta yi watsi da zargin tare da jaddada cewa kare kan ta ke tare da mai da martani kan harin mayakan Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban bara da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 1,200.