SiyasaIran
Iran ta soki rufe ofishinta na Jakadanci a Jamus
November 1, 2024Talla
Iran ta ce rufe wasu ofisoshinta na Jakadanci a Jamus da mahukuntan kasar suka yi tamkar takunkumi ne gwamnatin ta kakaba 'yan Iran da ke zaune a Jamus.
Hakan dai na zuwa ne bayan da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a ranar Alhamis ta sanar da cewa za a rufe ofisoshin jakadancin Iran guda uku da ke Jamus a matakin martani ga kisan wani Bajamushe da ke da asali da Iran Jamshid Sharmahd. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki lamirin matakin a wata kasida da ya wallafa a shafin Internet.
A halin da ake ciki kuma Jamus ta yi kira ga 'yan kasarta da ke Iran su bar kasar tare da yin gargadi ga Jamusawa su kiyayi zuwa kasar Iran.