IAEA: Iran ta kara yawan uranium dinta
July 8, 2019Darakta janar na hukumar Yukiya Amano ya shaidawa mambobin gudanarwa na hukumar cewa kawo yanzu Iran ta kara yawan makamashin nata zuwa sama da kaso hudu, kamar yadda ta shelanta a karshen mako da kanta. Rahoton ya kara da cewa sai dai har yanzu makamshin nata bai kai adadin kaso 20 da take sarrafawa gabanin yarjejeniyar ta 2015 ba kuma ba zai isheta ta sarrafa makaman kare dangi ba. Matakin na Iran dai na zuwa ne bayan da Amirka ta fice daga cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 tare kuma da kakabawa Tehran sababbin takunkuman karya tattalin arziki, inda Iran din ta bukaci kasashen Turai da su yi wani abu da zai taimaki tattalin arzikinta da ya tsunduma cikin rudani amma hakan ta gagara. A hannu guda kuma mataimakin shugaban kasar Amirkan Mike Pence ya sanar da cewa za su ci gaba da matsawa tattalin arzikin Iran din lamba tare kuma da shan alwashin kare muradun Amirkan a yankin Gabas ta Tsakiya.