1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta gayyaci jami'an IAEA

January 4, 2011

Iran ta gayyaci jami'an hukumar makamashin Nukiliya IAEA domin fayyace shirinta na nukiliya

https://p.dw.com/p/ztFb
Shugaban kasar Iran Mahmoud AhmadinejadHoto: AP

Iran ta gayyaci jakadun hukumar makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya su ziyarci tashoshinta na nukiliya domin gani da ido. Matakin dai ya zo ne yan makonni kalilan kafin taron kasashen Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Rasha da kuma Amirka wadanda ke shirin sake tattauna batun nukiliyar. Iran din na son ta nuna cewa da gaske ta ke kan tattaunawa game da shirinta na Nukiliya. Manyan kasashen na duniya dai na bukatar ganin Iran ta dakatar da shirin Nukiliyar ne dungurungum. Da dama daga cikin kasashen na zargin cewa Iran na fakewa ne domin kera makamin kare dangi lamarin da Iran din ta musanta tana mai cewa tana da cikakken 'yancin bunkasa makamashin Uranium domin samar da wutar lantarki ga al'umarta. A watan da ya gabata Iran ta gudanar da tattaunawa a birnin Geneva tare da wakilan kasashe biyar masu kujerar dundundun a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya tare da Jamus yayin da zagaye na biyu na tattaunawar za ta gudana a cikin wannan watan a kasar Turkiya.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita :  Umaru Aliyu