1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na kokarin janyo kasashen Afrika a jika

July 10, 2023

Shugaban kasar Iran zai fara ziyara a kasashe uku na nahiyar Afrika a kokarin tabbatar da sabbin manufofin kasar da ma kulla alaka da sabbin abokan hulda a nahiyar.

https://p.dw.com/p/4TgXn
 Videokonferenz | Putin - Raisi
Hoto: Iran's Presidency/WANA/REUTERS

A yayin ziyarar ta kwanaki uku da ke zama ta farko a cikin shekaru 11 da wani shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai kai nahiyar Afrika, Ebrahim Raissi zai gana da shugannin kasashen uku da suka hadar da Kenya da Yuganda da Zimbabuwe, domin kulla huldar diflomasiyya da kuma ta kasuwanci. 

Gabannin fara ziyarar, mai magana da yawun fadar Tehran Nasser Kanani, ya ce Iran na son janyo kasashen uku ne a jika domin suna da manufofin siyasa da ci gaba iri guda.

Iran din dai ta sallama wa kasashen Afirka ne a daidai lokacin da ta karfafa huldarta da kasashen China da Rasha, bayan kuma ta kawo karshen zaman tankiyar da ta kwashe shekaru bakwai tana yi da Saudiyya.