1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC: Yiwuwar dage zaben Najeriya

January 10, 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta ce ta yiwu a dage babban zaben kasar da za a gudanar a watan Fabarairun shekarar 2023 saboda matsaloli na tsaro.

https://p.dw.com/p/4LwIp
Yadda wasu ke kada kuri'a a Najeriya
Hoto: DW/K. Gänsler

Sakamakon fargabar tsaro da ake da ita a Najeriya, Hukumar zaben kasar ta ce ta yiwu a dage babban zaben da za a gudanar a wannan shekarar ta 2023. A cewar guda daga cikin shugabannin hukumar Abdullahi Abdu Zuru, idan har aka gaza shawo kan matsalar tsaro a Najeriya, babu zabin da ya wuce a dage zaben zuwa wani lokaci.

Shugaban ya kuma ce, gabanin zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabarairu, akwai bukatar a samarwa jami'an tsaro da kuma jami'an zaben isassun kayayyakin aiki domin tunkarar kowani irin kalubale. To sai dai kuma bangarori da dama a Najeriyar na tabbatar wa al'umma cewa za a samar da yanayi mai kyau domin gudanar da zaben bana cikin nasara.

Da dama dai na nuna fargaba yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsaloli na tsaro da kuma masu garkuwa da mutane. Ko a karshen makon da ya gabata, an yi garkuwa da wasu gomman mutane a tashar jirgin kasar da ke jihar Edo.