1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsalar tsaro na yin kamari

July 15, 2020

A yayin da suka cika shekaru biyar suna jan ragamar kokari na kai karshen rigingimu iri-iri a Tarayyar Najeriya, ra'ayi na bambanta bisa rawar manyan hafsoshin tsaron kasar, a cikin manyan yakoki guda biyu.

https://p.dw.com/p/3fNO9
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Har yanzu Najeriya na fama da masu ayyukan ta'andanci da 'yan bindiga dadiHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Duk da cewar dai ba sune mafi dadewa a bisa baban aikin jagorantar rundunoni na tsaron Tarayyar Najeriyar ba, daga dukkan alamu manyan sojojin kasar da ke bisa mulki yanzu na zaman mafi dauka na hankali cikin Najeriyar a lokaci mai nisa. A cikin wannan mako ne dai manyan hafsoshin guda hudu, suka cika shekaru biyar suna  jagoranci na rundunonin sojan kasar daban-daban.

Shekaru biyar da ke cike da hayaniya ga gwamnatin kasar 'yar sauyi da ta hau mulki na kasar a cikin fatan samun sauyin ga batun tsaron da ya nuna alamu na wucewa da sanin lemar PDP, da ta jagoranci kasar na shekaru dai-dai har 16.

Nigeria Katsina Sicherheit
Zanga-zangar rashin tsaro a KatsinaHoto: DW/H. Y. Jibiya

Duk da cewar daga farkon fari sun yi nasarar rage kere bama-bamai na masu ta'addar yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar, shekarun biyar dai sun rikide ya zuwa shekarun da ke kama da shekarun kuraye a kasar. An dai zargi gazawa an kuma kira mummunan cin hanci, ko bayan kokari na bore a tsakani na kananan sojojin da ke fadin ta yi baki ta lalace, bisa rashin kulawa ga sojojin da suke yakin. Ya zuwa yanzu dai ra'ayi na 'yan kasar na bambanta, kama daga kwararrun da ke tunanin ba daidai, ya zuwa shugabanni na garin da ke ganin ba sauyi a shekarun biyar.

Kara zurfin ramin rashin tsaro, ko kuma rawar 'yan mata cikin  batun rashin tsaron, hafsoshin dai sun share tsakanin shekaru 37 ga babban sojan kasa na kasar  ya zuwa 40  ga takwaransa dake jagorantar sojoji na sama. Shugaban kasar dai na fuskantar kari na matsin lambar kare wa'adin hafsoshin tare da bayar da damar zuba sabon lale a cikin fatan cin karfin jerin rigingimu walau na ta'addancin da ke Arewa maso Gabas, ko kuma 'yan ina da kisan da ke cin karensu har gashinsa a Arewa maso Yammacin kasar.