1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICJ ta umurci Isra'ila ta bude karin hanyoyin shiga Gaza

March 28, 2024

Kotun duniya ta umurci Isra'ila ta kara bude wasu hanyoyin da za a shigar da agaji zuwa Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/4eEjI
ICJ ta bukaci Isra'ila ta bude karin hanyoyin shiga Gaza
ICJ ta bukaci Isra'ila ta bude karin hanyoyin shiga GazaHoto: Remko de Waal/ANP/AFP/Getty Images

Kotun duniya ta umurci Isra'ila ta bayar da damar shigar da abinci da ruwa da man fetur da sauran kayan agaji zuwa Zirin Gaza da yaki ya daidaita. Kotun ICJ ya fitar da sabbin matakan na wucin gadi ne ga karar da Afirka ta Kudu ta shigar na zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza bayan da kungiyar Hamas ta kai mata hari a ranar 7 ga watan octobar bara, zargin da Isra'ilar ta musanta ta na mai cewa ta dauki matakan kare kanta ne.

karin bayani: Kotun duniya ICJ za ta fara sauraron shari'ar halascin mamayar da Isra'ila ta yi wa Falasdinawa 

Kotun ta kuma bukaci Isra'ila da ta gaggauta tabbatar da cewa dakarunta ba su aikata ayyukan take hakkin bil Adama ba ga Falasdinawa.

Umurnin kotun na wannan Alhamis din dai na zuwa ne bayan da kasar Afirka ta Kudu ta neman karin matakan kare fararen hula a Zirin da suka hada da tsagaita bude wuta da kuma magance matsalar bazaranar yunwa. Sai dai Isra'ila ta bukaci kotun da ta dakatar da bayar da sabbin umurni.