1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC za ta tura sammaci ga wasu 'yan Rasha

March 13, 2023

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC za ta tura sammaci ga wasu 'yan Rasha, bisa zargi da hannu cikin mamayar da kasar ta kaddamar a Ukraine da kuma laifukan yaki.

https://p.dw.com/p/4Od1a
Hoto: Peter Dejong/AP Photo/picture alliance

Ana dai sa ran mai shigar da kara ya nemi amincewar alkalin kotun kan tura sammacin kame jami'an, bisa zargin laifukan yin garkuwa da kananan yara daga Ukraine zuwa Rasha da aikata kisan gilla da kuma lalata gine-ginen fararen hula a kasar. Sai dai ma'aikatar tsaron Rasha ta ki amincewa da mayar da martani kan lamarin.

Wasu dai na ganin ta yiwu gwamnatin Moscow ta ki amincewa da sammacin sai dai kuma kotun ka iya kakaba mata tsauraran takunkumai.