SiyasaAfirka
ICC za ta yanke wa Ntaganda hukunci na karshe
March 30, 2021Talla
Tun a shekarar ta 2019 ne dai kotun da ke birnin Hague ta same shi da laifukan da suka hada da kisa da cin zarafin mata da kananan yara a lokacin da kungiyarsa ke tashen kaddamar da hare-hare a jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. A bisa wannan kotun ta yanke masa hukuncin shekaru 30 a gidan maza.
Sai dai Ntaganda wanda tsohon janar ne na soja da ya rikide ya koma dan tawaye ya musanta zarge-zargen, inda lauyoyinsa suka ce kotun ta ICC ta tabka kurarai a cikin hukuncin nata.
A shekarar 2013 dakarun gwamnatin Kwango suka murkushe kungiyar 'yan tawaye ta M23 da Ntaganda ya jagoranta kuma a wannan shekara shi da kansa Ntaganda ya yi saranda inda ya mika kansa ga ofishin jakadancin Amirka da ke birnin Kigali na Ruwanda.