1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IAEA: Iran ta zarta iyakancewa kan Uranium

Abdullahi Tanko Bala
September 4, 2020

Hukumar IAEA ta ce Iran mallaki adadi mai yawa na sinadarin Uranium da ya rubanya har sau goma akan adadin da aka iyakance mata a karkashin yarjejeniyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya

https://p.dw.com/p/3i1lK
Iran IAEA Inspektion in Natanz 2014
Hoto: Imago

Kamfanin dillancin laraban Jamus dpa ya ruwaito cewa zuwa watan Augustan 2020, Iran ta tara kimanin kilo 2,105 na sinadrin Uranium.

Yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015 da manyan kasashen duniya ya iyakance wa Iran kilo 202 ne kawai na Uranium domin ganin bata mallaki adadin da za ta iya kera makamin kare dangi ba.

Iran dai ta fara karya yarjejeniyar ce a bara domin martani ga kudirin Amirka na janyewa daga yarjejeniyar da kuma sake kakaba mata takunkumi.

Kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China na kokarin samun daidaito domin ceto yarjejeniyar daga rugujewa.

A halin da a ciki hukumar makamashin nukiliyar ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA ta ce Iran ta bada dama ga jami'anta bincike su ziyarci daya daga cikin cibiyoyi biyu na tashar nukiliyar domin tantance ayyukan da aka gudanar a tashar a baya bayan nan.