Saban shugabanci a hukumar IAEA
March 26, 2009Ɗaya daga cikin abubuwan dake addabar hukumar makamashi ta ƙasa da ƙasa IAEA shi ne yadda zata tinkari saɓanin da ake fama da shi tare da ƙasashe 'yan kama karya kamar Koriya ta Arewa, mai mallakar makaman ƙare dangi da Iran da ake zargi da ƙoƙarin mallakar fasahar sarrafa waɗannan makamai. Kawo yanzun dai hukumar sai lalube take yi a cikin dufu. Kuma ko da yake ba a cimma nasarar zaɓen sabon shugaban hukumar a ƙuri'ar da ta kaɗa a yau ba, amma manazarta sun haƙiƙance cewar duk sabon shugaban da za a naɗa zai ci gajiyar sabuwar manufar gwamnatin Amurka na kyautata dangantaka da Iran a diplomasiyyance.
Shugaba Barack Obama dai ya miƙa hannun musafaha. Sabon shugaban na Amurka na fatan shawo kan saɓanin da ake yi da ƙasar iran akan shirinta na nukiliya a cikin ruwan sanyi. Hakan ya fito fili a saƙonsa na bidiyo da ya aika wa Iraƙi don taya murnar sabuwar shekara, a makon da ya gabata.
Ya ce:Amurka na fatan ganin janhuriyar Islama ta Iran ta ɗauki matsayin da ya dace da ita a tsakanin ƙasashe. Wannan haƙƙi ne na ƙasar ta Iran, amma kuma yana tafiya ne da halin sanin ya kamata, ba za a iya cimmasa da ta'addanci ko ƙarfin bindiga ba, sai dai da laluma, wanda lamari ne da aka san Iranawa da shi.
Saƙon na Obama dai a lokaci guda tamkar haƙiƙancewa ne cewar manufofin da Amurka ke bi dangane da Iraƙi sun shiga hali na ƙaƙa-nika-yi. Ƙasashen Turai da Amurka na tuhumar gwamnatin Iran da yunƙurin fakewa da guzuma domin ta harbi karsana, inda take maganar samar da makamashin nukiliya, amma a haƙiƙa ƙoƙari take yi ta mallaki makaman ƙare dangi. Amma Rasha, a daura da haka, ba ta ga wata alamar dake nuna cewar shirin nukiliyar Iran na da nasaba da wata manufa ta soja ba. Ita kuwa hukumar makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa IAEA a taƙaice kawo yanzu ba ta da wata takamaimiyar masaniya a game da manufar Iran dangane da shirin nata na nukiliya. Sakatare-janar na hukumar ta IAEA Muhammad El-Baradei ya ce dalilin haka shi ne rashin ba da haɗin kai daga ɓangaren ƙasar ta Iran: Kafin a samu ci gaba mai ma'ana a wannan batu, wajibi ne Iran ba da cikakkiyar dama ta neman bayanai da wurare da kuma jami'an dake da hannu a wannan shiri.
Ta haka ne kawai za a amince da gaskiyar manufarta ta amfani da tashoshin nukiliyar don samar da makamashi a kuma soke takunkumin da aka garƙama mata. Ita dai hukumar ta IAEA tayi imanin cewar ƙasar Iran na ci gaba da tace ma'adanin uranium duk da takunkumin da kwamitin sulhu na MDD ya ƙaƙaba mata. Akan yi amfani da uranium da ba a tace sosai ba don samar da makamashi. Amma uranium da aka tsaftace shi sosai akan yi amfani da shi ne don ƙera makaman ƙare dangi. Rahotanni masu nasaba da hukumomin leƙen asirin Amurka dai sun nuna cewar kawo yanzun Iran ba ta tsaftace uranium don ƙera makaman nukiliya. Kuma ita kanta ƙasar na musunta zargin da ake mata na yunƙurin sarrafa waɗannan makamai, kuma ta dage akan 'yancinta na mallakar tashoshin makamashin nukiliya daidai da sauran ƙasashen dake da irin waɗannan tashoshi. To sai dai kuma akwai masu tababa cewar anya dai ƙasar ta Iran ba zata nemi mallakar makaman na ƙare dangi nan gaba ba. Domin kuwa mallakar waɗannan makamai zai ƙara ƙarfafa matsayin tsaron kanta. Bugu da ƙari kuma hakan zai kare makomar gwamnati daga masu ƙoƙarin kifar da ita daga waje. Babban misali game da wannan manufa ita ce Koriya ta Arewa, wadda tayi tsawon shekaru tana wasa da hankalin MDD da hukumar IAEA. A wani lokacin da amince da masu binciken tashoshinta, wani lokacin kuma ta ƙiya ƙememe, har ya zuwa shekara ta 2006, inda fadar mulki ta Pyongyang ta sanar da duniya cewar ta gwada makaminta na nukiliya. Kuma ko da yake akwai masu tababa a game da cewar ƙasar na mallakar makaman ƙare-dangi, amma fa aƙalla an samu raguwar barazanar da take fuskanta daga ƙetare.
Mawallafi:Nils,Naumann/ Ahmad Tijani Lawal.
Edita: Yahouza Sadissou