1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

I S ta dau alhakin harin Yemen

Abdul-raheem Hassan
November 5, 2017

Kungiyar ta sanar da ikirarin kai harin a shafin ta na Internet, harin da ya yi sanadiyar mutuiwar Sojojin gwamnati bakwai a birnin Aden da ke yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/2n3WE
Somalia Mehrere Tote bei Anschlag mit zwei Fahrzeugbomben in Mogadischu
Hoto: Reuters/F. Omar

Harin farko dai ya faru ne a yayin da dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa da bam a cikin wata mota makare da ababen fashewa a wani shingen binciken jami'an tsaro, yayin da hari na biyu ya auku yayin da 'yan bindigan cikin kayan Sojoji suka yi luguden wuta da bama-bamai kan wasu gine-ginen gwamnati a birnin Aden.Bam ya kashe Sojoji biyar a Yemen

Dama dai birnin Aden na cike da Sojojin Saudiyya da ke talafawa dakarun gwamnatin Yemen yakar 'yan tawayen Houthi da ke ja in ja da gwamnatin shugaba Abdrabbuh Mansur Hadi.

Wannan harin na zuwa ne kwana guda bayan da mayakan Houthi suka kai wa kasar Saudiyya hari da makami mai linzami da ya fadi kusa da filin jirgin saman birnin Riyadh, harin da gwamnatin Saudiyyan ta ce dakuran ta sun dakile shi ba tare ya haddasa wata asara ba.Yemen ta nemi agajin kasashen duniya