1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dankantaka tsakanin Falasdinu da Isra'ila

November 18, 2020

Hukumar zartaswa ta Falasdinu OLP ta ba da sanarwar sake kulla hulda da Isra'ila. Jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce su za su sake  kulla huldar daga inda aka tsaya.

https://p.dw.com/p/3lTlm
Bildkombo Benjamin Netanjahu und Mahmud Abbas
Benjamin Netanyahu a hannu hagu da Mahmoud Abbas a hanu damaHoto: Reuters/C. Allegri

Tun farko Falasdinu ta dakatar da huldar ne sakamakon  ci gaba da giggina matsauguna Yahudawa a gabar yamma da Kogin Jordan da Isra'ilan ta yi. Matakin da Falasdinu ta dauka na katse huldar ya janyo dakatar da jinyar marasa lafiya Falasdinawa a cikin asibitocin Isra'ila, sanann Isra'ila ta soke bai wa hukumar Falasdinawan kudaden haraji da take karba daga jama'ar Falasdinu.