1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 13 da faduwar jirgin saman Yemen

Ramatu Garba Baba
September 14, 2022

Sama da shekaru goma da faduwar jirgin saman kasar Yemen, kotu a Faransa ta shirya yanke hukunci a shari'a da ake kan zargin sakaci a faduwar jirgin fasinjan.

https://p.dw.com/p/4Gos6
Jemen Luftangriff auf dem Flughafen in Sanaa
Hoto: Reuters/K. Abdullah

A wannan Larabar, wata kotu a kasar Faransa ke yanke hukunci kan shari'ar da aka jima ana yi da kamfanin jirgin gwamnatin Yemen da aka zarga da amfani da matuka jirgin da ba su da kwarewa. Jirgin ya fadi ne a shekarar 2009 inda duk fasinjojin 152 da ke ciki suka mutu, yarinya guda yar shekaru goma sha biyu ce kadai, ta tsira daga mummunar hadarin jirigin da ya auku a watan Yunin shekarar 2009.

Jirgin ya taso ne daga birnin Sanaa babban birnin kasar Yemen kafin ya fadi a tsibirin Comoros, masu bincike sun ce, sun gano cewa, duk na'urorin cikin jirgin na aiki da kyau, amma matukan jirgin ne ba su da kwarewar da ta dace, kuma a kai ake tuhumar kamfanin jirgin. Akasarin wadanda suka mutu a hadarin jirgin Faransawa ne, kuma danginsu sun kai kamfanin kotu inda suka ci gaba da fafutukar ganin an musu adalci ta hanyar hukunta kamfanin jirgin bisa sakacin da ya janyo asarar 'yan uwansu.