1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta kama kawun Bashar al-Assad d laifi

Abdoulaye Mamane Amadou
June 17, 2020

An yanke hukuncin zaman gida kaso na tsawon shekaru hudu ga kawun shugaban Siriyya Bashar al-Assad mai suna Rifaat al-Assad tare da karbe wasu kaddarorin da ya mallaka.

https://p.dw.com/p/3dwlZ
Assads Onkel | Rifaat al-Assad
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/M. Euler

Wata kotu a birnin Paris ta yanke hukuncin daurin gidan yari har na tsawon shekaru hudu ga Rifaat al-Assad wani kawun shugaban kasar Siriyya Bashar al-Assad

Sai dai ko baya ga hukuncin zaman gidan yarin, kotun ta kuma yanke hukuncin karbe kaddarorin da Rifaat al-Assad mai shekaru 82 a duniya, ya tara wadanda aka kiyasta sun kai euro miliyan 90, to amma bisa rashin lafiyarsa an yi shara'ar ce ba tare da halartar Rifaat a gaban kotun ba.

Tuni dai lauyoyin da ke kare shi suka yi kakkausar suka ga matakin suna cewar ba a yi masa adalci ba kuma za su daukaka kara.