1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Tarrayar Najeriya na ƙoƙarin tabbatar da tsaro

May 15, 2013

Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar taɓaci a cikin wasu jahohin yankin arewacin ƙasar guda ukku: Waɗanda suka hada da Borno da Adamawa da kuma Yobe.

https://p.dw.com/p/18Xpg
Nigerian President Goodluck Jonathan speaks during a nationwide live broadcast on the state television on May 14, 2013. President Goodluck Jonathan has declared state of emergency in the nation's troubled northeast states of Yobe, Borno and Adamawa, where Islamic extremists now control some of the country's villages and towns, promising to send more troops to fight what is now an open rebellion. AFPPHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A cikin jawabin da ya yi ta kafofin yaɗa labarai na ƙasar shugaban ya ce, ya ayyna wannan doka ce  saboda rashin tsaron da ake fama da shi. Na yan ƙungiyar Boko Haram wanda kawo yanzu lamarin ya janyo  asarar ta rayukan jama'a da dama tun lokacin da aka fara rikicin a shekarun 2010 kuma shugaban ya kara da cewar.

Ya ce :'' Bayyanai da na samu daga jam'ian tsaron mu,ƙsasar mu na fuskantar lamari ne, na ta'addanci wanda ke buƙatar ɗaukar rin wannan mataki.'' Gwamnatin Tarrayar dai za ta aike da ƙarin sojoji a jahohin, waɗanda harkokin tsaro za su koma a ƙarƙashin jagorancin soji. A shekarun 2004  da kuma 2006  tsohon shugaban gwamnatin mulkin  farar hula Olusegun Obasanjo ya taɓa ɗaukar irin wannan doka a jahar Filato tare da dakatar da gwamnoni yanki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita        : Halima Balaraba Abbas