Hukumomin Tarrayar Najeriya na ƙoƙarin tabbatar da tsaro
May 15, 2013A cikin jawabin da ya yi ta kafofin yaɗa labarai na ƙasar shugaban ya ce, ya ayyna wannan doka ce saboda rashin tsaron da ake fama da shi. Na yan ƙungiyar Boko Haram wanda kawo yanzu lamarin ya janyo asarar ta rayukan jama'a da dama tun lokacin da aka fara rikicin a shekarun 2010 kuma shugaban ya kara da cewar.
Ya ce :'' Bayyanai da na samu daga jam'ian tsaron mu,ƙsasar mu na fuskantar lamari ne, na ta'addanci wanda ke buƙatar ɗaukar rin wannan mataki.'' Gwamnatin Tarrayar dai za ta aike da ƙarin sojoji a jahohin, waɗanda harkokin tsaro za su koma a ƙarƙashin jagorancin soji. A shekarun 2004 da kuma 2006 tsohon shugaban gwamnatin mulkin farar hula Olusegun Obasanjo ya taɓa ɗaukar irin wannan doka a jahar Filato tare da dakatar da gwamnoni yanki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas