hukumar nukiliya ta IAEA ta soki gwamnatin Amurka
September 14, 2006Talla
Hukumar kula da kare yaduwar makaman nukiliya ta soki gwamnatin Amurka game da rahoton da majalisar kasar ta fitar wanda ya nuna cewa,kasar Iran ta inganta uraniyum fiye da yadda supetocin Majalisar Dinkin Duniya suka baiyana.
Hukumar ta baiyana rahoton da cewa bai baiyana gaskiya ba kuma ya wuce gona da iri.
Cikin wata takarda dake nuna bacin ran majalisar,jamianta sunce, jamian leken asiri na Amurka sunyi kuskure cewa Iran ta inganta sinadaren uranayium zuwa matsayin makamai,wadda a hakikanin gaskiya abinda hukumar ta gano bai kai yadda jamian na Amurka suka baiyana ba.
Tun a 2003 ne dai supetocin MDD suke sa ido kan shirin nukiliya na Iran wanda har ya zuwa yanzu basu gano wata alama da ke nuna cewa Iran tana kera makaman kare dangi ne ba.