1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta yi watsi da bukatar da Iran ta miƙa mata.

November 23, 2006
https://p.dw.com/p/Buah

Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato IAEA, ta ce ta yanke shawarar yin watsi da bukatar da Iran ta gabatar mata, ta neman taimakonta wajen gina tashar samad da makamashin nukiliya. Bisa wannan shawarar da hukumar ta yanke dai, ba za a takalo bukatar ta Iran ba kuma ke nan a tarukanta, har sai bayan shekaru biyu nan gaba. Iran ɗin za ta iya sake miƙa bukatarta ne bayan tsawon wannan lokacin. Hukumar dai ta sha yi wa Iran kira, na ta dakatad da gina tsahar makamashin nukiliyanta a garin Arak, mai nisan kimanin kilomita ɗari 2 a kudu da birnin Teheran.