1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta yanke shawara gurfanar da Iran gaban komitin sulhu

Yahouza SadissouMarch 8, 2006

Bayan kwanaki 3 na mahaura, hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukleya ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta yanke shawara gurfanar da Iran gaban komitin sulhu.

https://p.dw.com/p/Bu1E
Hoto: AP

A tsawan kwanaki 3 mahalarta wannan taro, sun tabka mahaurori masu zafi, a game da batun rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, wanda a halin yanzu a ke ta faman kai ruwa rana a kai a fagen diplomasiar dunia.

Wakilan, sun yi nazari a kan rahoton da shugaban hukumar IAEA, Mohamed EL Baradei ya gabatar a sakamakon binciken da ya gudanar a Iran.

A farkon watan februabu da ya gabata, hukumar IAEA ta baiwa Iran saban wa´adin wata guda, domin watsi da aniyar ta, ta ƙera makamin nuklea.

Rahoton da Mohamed El baradei ya gabata,r ya nuna ƙara ƙara cewa, hukumomin Iran, sunyi kunnen uwar shegu da wannan wa´adi.

Sakamakon mahaurorin kwanaki 3, da aka tabka, a birnin Vienna,wakilan sun ce, yanzu hanya ɗaya tilo, da ya rage itace, gurfanar da Iran, gaban komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Jim kaɗan bayan kammala zaman taron, mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amirika, Nicholas Burns ya tabbatar cewa,ranar litinin ko talata mai zuwa, za a shigar da ƙaran na Iran, gaban komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Amurika da ƙungiyar gamayya turai, sun bayana cewar bayan lallasin Iran da su ka yi,yanzu lokaci yayi,na ɗaukar mattakan hukumta ta, a game da matsayin da ta ɗauka na rena dunia ta hanyar share kiran da ƙasashe ke ci gaba da yi mata, na dakatar da ayyukan ƙera makamin Nuklea.

Saidai Wani kurrare ta fannin harakokin diplomasia, da ya halarci taron na Vienna, ya sanar kaffofin watsa labarai cewa, gurfanar da Iran gaban komitin Sulhu mataki ne irin na kada mage ba yanka ba.

Wato hakan, bai nufi da a nan take, komitin sulhun, ya ɗauki mattakan hukumta Iran, ta la´akari da yada, humomin wannan ƙasa ke da goyan baya daga ƙasashe kamar su Rasha, China, da ma a fakaice wasu ƙasashen turai.

A ta bakin Paul Rogers na jami´ar Bradford dake Britania, kuma massani ta fannin diplomasia, batun ɗaukar mattakan hukunci a kann Iran, abu ne da kamar wuya, sai dai kawai a ci gaba da kai ruwa rana, har lokacin da a ka samu nasara ciwo kan taƙƙadamar.

A nasu gefe, hukumomin Iran, tunni, sun maida martani ga wannan mataki, da hukumar IAEA ta yanke, da cewar babu gudu babu ja da baya.

Saidai, wakilin Iran, a hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukleya,Ali Asghar Sultania, ya ce za su ci gaba da bada haɗin kai, ga hukumar, duk da wannan mumunan hukunci da ta yanke.