HUKUMAR IAEA TA WANKE IRAN AKAN KERA MAKAMAN NUCLEAR.
November 15, 2004A jiya ne hukumar kula da yaduwar Nuclear ta mdd tayi kwaerkwaryanwanke kasar Iran,dangane da zargin da ake mata na yunkurin kera makamai da sinadarin Uranium,yini guda bayan da Tehran ta yiwa turai alkawarin dakatar duk wata harka data shafi sarrafa sinadaran na Uranium.
Jamian diplomasiyy sun bayyana cewa wannan wata nasara ce a banagaren ita Iran,wanda kuma a daya hannun zai kasance abu mawuyaci wa Amurka ta gabatar da ita gaban kokitin sulhun mdd kamar yadda ta nema a wannan wata da muke ciki.
To sai dai hukumar kula da yaduwar makaman Nuclear watau IAEA a takaice ,bata watsi da zargin da Amurkan kewa Iran dangane da kera makamai a asirce ba.Domin kwantar da hankalöin duniya kann wannan batu Iran tayi alkawarin dakatar da sarrfa sinadarin Uranium daga ranar 22 ga watan Nuwamba,wanda ke bangaren yarjejeniyar data cimma da kungiyar gamayyar turai EU,domin kaucewa takunkumin komitin sulhu na mdd.
A wani rahoto da hukumar ta IAEA ta fitar a jiyan,tayi nuni dacewa bazata iya cewa ita Tehran ta gabatar da dukkan bayanai da ake bukata kann sinadran ta na Uranium ba,sai dai ta gabatar da wadanda aka tabbatar dacewa basu da illa.
Ita dai Iran mai arzikin albarkatun man Petur,ta sha nanata cewa tana amfani da sinadran na Uranium wajen samarwa alummar ta wutan lantarki.A dangane da haka ne hukumar ta IAEA ta gudanar da bincike a kann wannan batu na zargin cewa tana iya amfani dasu wajen kera boma bomai.Ana dai kyautata zato nan gaba ne shugaban hukumar Mohammed Elbaradei zai gabatara da rahoto na karshe dangane da sakamakon wannan bincike.
A halin da ake ciki yanzu dai hukumar ta IAEA tace zata cigaba da gudanar da bincike a dangane da halin da Tehran din ke ciki a game da wannan zargi da ake mata na sarrafa sinadaran Uranium domin kera makaman Nuclear,domin a yanzu bata shaida na tabbatar da hakan.
Amurka dai bata yarda da Iran ba ,domin tayi imanin cewa tana kera makaman nuclear a asirce.
A watan oktobar data gabata ne dai Hukumomin Iran da kungiyar gamayyar turai suka cimma yarjejeniya makamancin wannan,amma watanni shida bayan nan aka rusa wannan yarjejeniya.
Koda yake wannan rahoton na hukumar Nuclear na bayanin binciken da aka gudanar cikin shekaru 2 da suka gabata ne,akwa wasu sabbin batutuwa da suka taso.