Hukumar IAEA ta tasa keyar Iran izuwa gaban Mdd
March 8, 2006Talla
Hukumar zartarwar kula da makamashin nukiliya ta duniya , wato IAEA ta amince da tasa keyar kasar Iran izuwa Mdd, don sanin matakin daya mkamata dauka a kanta.
Daukar wannan mataki dai ta hanyar tura rahoton hukumar kann kokarin da kasar ta Iran keyi na mallakar makamin na Aton yazo ne bayan wakilan hukumar 35 sun kammala kalailaice shi.
A dai mako mai zuwa ne ake sa ran kwamitin sulhu na Mdd zai fara gudanar da taron sa don sanin matakin daya kamata a dauka akan kasar ta Iran.
Kafin dai daukar wannan mataki, mahukuntan Amurka sun yi watsi da kurarin da kasar Iran tayi na cewa matukar an kai karar ta gaban kwamitin sulhu na Mdd, to kasar Amurka zata fi ko wace kasa a duniya dandana kudarta.