Hukumar IAEA ta gamsu da shirin Koriya ta arewa
June 29, 2007Talla
Hukumar makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya tace ta gamsu da ziyarar gani da ido da jamián ta suka kai kasar Koriya ta arewa bisa aniyar ta ta kwance shirin ta na nukiliya. A wata sanarwa da hukumar ta bayar bayan da jamián ta suka ziyarci cibiyar nukiliyar ta Pyonyang, tace ta gamsu da yunkurin koriya ta arewan na martaba yarjejeniyar da aka cimma da ita na rufe tashar nukiliyar inda kuma zaá sakanya mata da gudunmawar agaji kamar yadda yarjejeniyar ta tanada. Ziyarar Jamián hukumar makamashin nukiliyar ta majalisar dinkin duniya, ita ce ta farko tun bayan da Pyonyang ta kori jamián a watan Disamba na shekarar 2002