1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta fara taronta da zummar lakabawa Iran takunkumi

March 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5n

Hukumar kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa ta fara taronta yau a Vienna,wanda zai iya yanke shawara akan lakabawa kasar Iran takunkumi.

Kodayake a gobe talata ne ko laraba ake sa ran tattauna batun na Iran.

Sai dai shugaban hukumar Muhammad El-Baradei,ya baiyana imaninsa cewa zaa samu nasarar shawo kann kasar ta Iran ta dakatar da bincikenta na nukiliya.

Mahalarta taron membobi 35 sunce duk wani mataki da zasu dauka kann Iran din ba zai wuce takunkumi ba,amma El Baradai yace zaa iya kaucewa takunkumin muddin dai an cimma nasara a tattaunawar Iran da Rasha game da sarrafawa Iran din sinadarenta a Rasha.

Sai dai kuma jamian diplomasiya sun baiyanawa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa,akwai yiwuwar amincewa Iran ta gudanar da aiyukan inganta uraniyum din da bai wuce kima ba a cikin kasarta.