Hukumar IAEA ta fara cire kyamarorinta a tashoshin nukiliyar Iran
February 12, 2006Talla
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya rawaito cewar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta cire da yawa daga cikin kyamarorin da ta kakkafa a tashoshin nukiliyar Iran, bisa kiran da gwamnatin Teheran ta yi na a yi haka. Kamfanin dillancin labarun ya rawaito majiyoyin ´yan diplomasiya a hedkwatar hukumar IAEA dake birnin Vienna na cewa yanzu hanya guda daya ta ragewa hukumar na gudanar da bincike a tashoshin nukiliyar na Iran. Iran ta bukaci a cire makullayya da kuma kyamarorin bayan da hukumar IAEA ta yanke shawarar yin karar Iran din a gaban kwamitin sulhu na MDD. A jawabin da yayi wa taron gangamin tunawa da juyin juya halin Islama na 1979 a birnin Teheran, a jiya asabar shugaba Mahmud Ahmedi Nijad ya yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar da ta hana yaduwar makaman nukiliya a duniya.