Samar da sana'a ga nakasassu
April 14, 2021Kimanin matasa mabarata guragu 70 ne, wanda wani matashin Kaduna injiniya wanda shi ma gurgun ne mai suna Isiyaku Musa Ma'ayi ya horas da ‘yan uwansa nakasassu sana'ar walda da kere-keren kofofin zamani da kekunan hawa da baburan nakasassu dan dogaro da sana'ar hannu maimakon yawo da kokan bara kan titunan Kaduna
Isiyaku ya kara da cewa akwai sana'o'i da dama da ya kamata suna yi, to amma akwai bukatar fargar da su mahinmancin koyan wani sana'a dan rufawa kansu asiri. Burin shi ne na ganin an rage yawan matasa da ke bara, saboda kama sana'ar hannu,
Ya ce akwai wurare masu yawa da suke horas da su, kuma daga ciki kullun suna samun karuwar yawan matasa guragu daga birane da karkara da ke zuwa koyan sana'ar walda dan yin ban-kwana da bara da ke damun hukumomi da sauran kungiyyoyin jama'a na Nijeriya
Daga cikin kalubalen da yake fuskanta akwai dai na rashin sayen kayan nakasassu da kuma rashin tallafi daga hukumomi da attajiran kasa dan karfafa masu wannan sana'ar. Wani matashin gurgu daga cikin wadanda ake horas da su ya nuna jin dadi bisa irin sauyin rayuwa da ya samu.