Hirar Putin da manema labaru
February 1, 2007Talla
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya jaddada cewa,zaa zabi wanda zai maye gurbinsa ta hanyar zabe na democradiyya a karshen waadinsa.Sai dai a taron manema labaru na shekara shekara daya gudanar a birnin Moscow,Putin ya bayyana cewa yana da yancin bayyana goyon bayansa wa Dantakara daya fi so a yakin neman zabe...........
Shugaba Putin wanda zai sauka daga karagar Mulki a watan maris ya kuma karyata zargin cewa Rasha na amfani da matsayinta na mallakan albartkatun makamashi na ,na cimma wasu burinta na ketare.Kasar ta Rasha dai ta katse samar da iskar gas wa kasashen Belarus da Ukraine,na gajeren lokuta sau biyu a shekarar data gabata,adangane da bukatunta na karin farashi wa kasahen.